Advertisment

Zan Iya Saduwa Da Mai Haila Da Condom.

Advertisment

A

Wannan ranar munyi wayyace akan wata tambaya wanda wasu bayin Allah sukayi akan mutum zai iya saduwa da matarsa lokacin da take period wato jinin al’ada.

 

 Zoomfe sunyi kokarin samun tabbacecceyar answer Wanda wani malamin addinci Muslim ya bayar akan wannan tambayar

Advertisment

 

 Wannan amsa Kai tsaye shine Haramun ne, anma batun ansa Condom ga Amsar nan ????

 

Tambaya:

Advertisement

 

Assalamualaikum. Malam Allah ya karama daukaka da imani malam Allah ya jikan Iyayen mu da Imani malam  ga tambayata: shin mutum zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa Condom?

 

Wa’alaikum Salam

 

Amsa:

 

To dan’uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum ko duk wani Nau’in abinda yayi kama da haka saboda Allah ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma yın wanka.

 

Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za’a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condum .

Share to
You May Also Like
Advertisment