Advertisment

Masha Allah Yadda Aka Gudanar Da Walimar Haddar Al-qur’ani Yar Gidan Abba El-mustafa

Advertisment

An Gudanar Da Walimar Saukar Alƙur’ani Na ‘Yar Shugaban Hukumar Tace Fina Finai Na Jihar Kano Kuma Jarumi A KannyWood El-Mustapha, A Ranar Lahadi, 22 Ga Oktoba, 2023 aka yi taron walima na saukar karatun Alƙur’ani na ‘yar Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, wato Aisha Abba El-Mustapha (Lateefa).

Taron ya gudana da yamma a gidan El-Mustapha da ke Titin Malam Aminu Kano, kusa da Ƙofar Gadon Ƙaya, a birnin Kano, A wajen taron, wanda ‘yan’uwa da abokan arziki da dama su ka halarta, an yi karatun Alƙur’ani tare da addu’o’i, sannan kuma aka raba kyaututtuka ga yara. Ita ma amaryar saukar, wato Aisha, ta gabatar da karatu.

Cikin Alfahari Shugaban hukumar tace finafinai abba almustapha ya wallafa Hotunan Taron A Shafin Sa Na Sada Zumunta

Share to
You May Also Like
Advertisment