Advertisment

Karon 1: Sadiya Haruna Ta Maka G-Fresh A Gaban Kotu

Advertisment

Labaran Kannywood Sadiya Haruna Ta Maka mijinta wato G-Fresh Al’ameen Wanda akafi sani Kano state material a Gaban Kotu.

 Rigimar da ke tsakanin Sadiya Haruna da mijinta Abubakar Ibrahim (G-Fresh) ta kai su ga zuwa gaban kotu Tsohuwar jarumar ta Kannywood ta maka G-Fresh a gaban kotu tana neman a datse igiyar auren da ke tsakaninsu G-Fresh ya tubure yana son matarsa inda alƙalin kotun ya ƙara musu lokaci domin su je su sasanta tsakaninsu.

Zoomfe yayi bincike yadda lamarin ya kasance a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka! Jihar Kano – Shahararriyar tsohuwar jarumar Kannywood, Sadiya Haruna, ta maka mijinta, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kano tana neman, a raba igiyar auren da ke tsakaninsu. 

Advertisment

Jarumar, wacce aka fi sani a TikTok da Sayyada Sadiya Haruna, ta ce ta fahimci cewa mijin nata ba irin wanda take so ba ne, kuma ba za ta iya ƙarasa sauran rayuwarta tare da shi ba Read 

Idan ba a manta ba dai, auren da aka yi tsakanin jaruman na TikTok biyu ya ja hankalin jama’a saboda yadda aka yi ta cece-kuce a kansa. Yayin da G-Fresh ke zarginta da yin aboki namiji (Besty) wanda ba za ta iya rayuwa ba sai da shi, Sadiya ta ce maganar auren da ke tsakaninsu ta zo ƙarshe. 

Wacce buƙata Sadiya take da ita?

A yayin zaman kotun, Sayyada Sadiya Haruna ta hannun lauyanta Barr. A.B Saka ta buƙaci a raba aurenta da G-Fresh. Lauyan ya shaida wa kotun cewa a zaman farko kotun ta bayar da izini ga wanda ake ƙara ya nemi afuwar ta amma bai yi ba. 

A nasa ɓangaren lauyan G-Fresh, Salihu Umar Kududuffawa, ya shaida wa kotun cewa sun daɗe suna neman ta domin su daidaita auren amma ba a same ta ba. 

Advertisement
Share to
You May Also Like
Advertisment