Advertisment

Hukumar INEC Ta Janye Daukaka Karar Da Ta Yi Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Kano

Advertisment

Jihar Kano – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan kano ta yanke.

 

 An tabbatar da hakan ne a wata wasiƙa mai dauke da sa hannun Suleiman Alkali, shugaban sashin shari’a na hukumar a Kano, a ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba

Advertisment

 

INEC ta ɗaukaka ƙara Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shigar da ƙara kan hukuncin kotun, inda ta ce kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yi kuskure a cikin doka inda ta ayyana ɗan takarar masu shigar da ƙara, wanda ba ya cikin ƙarar a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

 

Idan za’a tuna a ranar litinin 29 ga watan mayu ne aka rantsar da gwamna Yusuf bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kano, kuma hukumar zaɓe ta miƙa masa takardar shaidar cin zabe.

Advertisement

Abba Ya Dauko hayar Lauyan Tinubu a wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauko hayar lauyan da ya kare Tinubu a shari’ar zaɓen.

Shugaban ƙasa. Wole Olanipekun zai kare gwamnan a ƙarar da ya ɗaukaka bayan kotun zaɓen gwamnan Kano ta ƙwace nasararsa a matsayin gwamnan kano.

Share to
You May Also Like
Advertisment