Advertisment

Gwamnatin Jihar Kano zata Fara Bawa Dalibai Mata N20,000 Duk Wata

Advertisment

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta fara bayar da tallafin Naira 20,000 ga ɗalibai mata 45,000 domin tallafa wa ilimin ƴaƴa mata tare da ƙarfafa gwiwar iyaye su tura ƴaƴansu mata zuwa makaranta.

 Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ƴancin kai wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano 

Abba Gida-Gida zai gina sabbin makarantu Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin sa tana kuma gina sabbin makarantu a fadin kananan hukumomi 44 a ƙoƙarin da suke yi na ganin sun kwashe duk yaran da ba su zuwa makaranta da ke yawo a kan tituna 

Advertisment

Hakazalika, ya nanata ƙudirinsa na tura dalibai 1001 da suka kammala karatun digiri na farko da daraja ta ɗaya zuwa ƙasashen waje domin yin digiri na biyu.

Gwamnatin Kano Za Ta Daukaka Kara A wani labarin na daban kuma, gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu na umartarta ta biya ƴan kasuwa diyyar N30bn. Wata babbar kotun tarayya dai ta umarci gwamnatin jihar da ya biya ƴan kasuwan da ta rusawa shagunansu a filin masallacin Idi, diyyar N30bn bayan sum maka gwamnatin ƙara a gabanta.

Share to
You May Also Like
Advertisment