Advertisment

Dalilin Da Yasa Aka yanke sojan Najeriya janar umar mohammed hukuncin shekara bakwai 

Advertisment

An kama Janar Umaru Mohammed da laifin satar sama da dala miliyan biyu da kuma sama da naira biliyan daya.

Kotun Sojin Nijeriya da ke zama a Abuja ta yanke wa wani babban jami’inta Manjo Janar Umaru Mohammed hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai.

Shugaban Alkalan sojin wanda ya jagoranci zaman shari’ar, Manjo Janar James Myam ya samu babban sojin da laifuka 14 cikin 18 da ake zarginsa da su.

Advertisment

Kamar yadda jaridar TRTAFRIKA na ruwaito,Kotun sojin ta bukaci Janar James ya mayar da dala 2,178,900 da kuma naira biliyan 1.65 ga Kamfanin Kadarorin Rundunar Sojin Nijeriya.

Laifukan da ake zarginsa da su sun haɗa da sama-da-fadi da kudade da kitsa tuggu da yin jabun takardu da karkatar da wasu kadarorin rundunar sojoji da kuma wasu sauran laifukan.

Kafin yanke hukuncin, Janar Mohamed na tsare a wani kwarya-kwaryan gidan yarin soji da ke Barikin Mogadishu a Abuja na wasu shekaru.

Lauyan da ke kare wanda ake karar Lekan Ojo ya bukaci a tura babban sojin da aka yanke wa hukunci zuwa Gidan Gyaran Hali na Kuje, sai dai alkalan na soji sun ki amincewa da hakan.

Advertisement

Manjo Janar Mohammed a baya ya kasance wanda ya jagoranci Kamfanin Kadarorin Rundunar Sojin Nijeriya.

Share to
You May Also Like
Advertisment