Advertisment

Aiki Da Cikawa: Gwamnatin Kano Ta Hana Amfani Da Wasu Littattafai A Makarantun Jihar

Advertisment

Gwamnatin jihar Kano ta hana koyar da wasu littattafai a daukacin makarantun jihar, har ma da na masu zaman kan su

Hakan ya biyo bayan tunasarwa da bangarori daban-daban sukai kan wasu illoli da suke cikin litattafan da ake ganin sunci karo da koyarwar Islama da al’adar jihar.

Hukumar Kula da Makarantu masu zaman kansu ce ta fitar da sanarwar mai dauke da sa hannun Hamisu Muhammad, Daraktan Tsare-tsare da bincike, a madadin Mai baiwa Gwamna Shawara kan Makarantu Masu Zaman Kansu, Baba Abubakar Umar.

Advertisment

Litattafan da aka haramta sun haɗa da The Queen Primer (dukka wallafar su), A Royal Series na kamfanin Nelson Publishers Limited, Basic Science for Junior Secondary School da kuma Razat Publishers, 2018 edition. (for JSS3).

Sauran sun hada da Active Basic Science wallafar 2014 na Tola Anjorin, Okechukwu Okolo, Philias Yara, Bamidele Mutiu, Fatima Koki, Lydia Gbagu, Basic Science & Technology for Junior Secondary Schools 1, 2 and 3: By W.K Hamzat, S. Bakare.

Sauran kuma su ne New Concept English for Senior Secondary Schools for SSS2, Revised edition (2018 edition) by J Eyisi, A Adekunle, T Adepolu, F Ademola Adeoye, Q Adams and, J Eto, da kuma Basic Social Studies for Primary Schools by BJ Obebe, DM Mohammed, S N Nwosu, J A Adeyanju and ah Carbin.

A na shi ɓangaren, Shugaban Hukumar Tace Fina-finai da dab’i ta jihar Kano, Abba El-Mustapha ya ce sun yi nasarar kama tarin littafin Queen Primer da gwamnatin ta haramta koyar dashi a fadin jihar Kano.

Advertisement

A jawabinsa, Abba El-Mustapha yace littafin Queen Premier yana koyar da yara fasadi da sauran dabi’un da suka sabawa addinin musulunci, wanda hakan ya sabawa al’adun bahaushe.

Share to
You May Also Like
Advertisment