Advertisment

Abubuwa 5 Da Zasu Gyara Zaman Aure Daga Sheikh Ibrahim Khalil

Advertisment

Shahareren malami addinin islama wata shiek Ibrahim Khalil tsohon Dan takarar gwamnan kano yayi jawabi akan wasu dalilai Wanda suke gyara rayuwar aure

A cikin wannann shekarar ansamu kashe kashen aure wanda yaninka na wacce shekarar shine babban malamin addinci Muslim yayi akan wasu dalilai wanda zasu gyara mana zaman aure sune kamar haka:

• Hakuri
• Kalmomi masu kyau
• Ana hakuri da juna( A daina kaiwa iyaye Kara)
• Fahimtar juna
• Yake hukunchi lokacin fushi.

Advertisment

•Hakuri: Kamal haƙuri ne ke riƙe aure mijji da mata su zama masu haƙuri da juna. Miji ya daina garaje wajen yin saki, ita kuma mace ta daina hasala wannan shine abunda zai saka aurensu ya zauna lafiya wato hakuri da juna dole sai kowa yayi hakuri da wani.

• Kalmomi masu kyau: Abu na biyu shine Kalmomi masu kyau lallai ne miji ya sani cewa kalmomi masu daɗi ne ke zaunar da aure lafiya. Ya dinga yabonta, yana ziga ta, yana koɗa ta, yana tausasa mata haka ita mata dole tana yiwa mijinta kalamae masu dadi kamar inasonka, ina ji da dakae DSS.

“Musamman a yanzu da ake cikin wani hali, ya dinga ba ta haƙuri, yana kwantar mata da hankali.”

• Daina kai wa iyaye ƙara: wanna babbar matsalace Wanda take lalata aure sosae lallai ne su daina kai wa magabatansu ƙara, su daina saka wani mutum na uku a tsakaninsu a harkar aure duk abunda sukayi suna zama tare suna yin sulhu kamar wani yaji sirrin aurensu.

Advertisement

• Fahimtar juna: Abin da ke zaunar da aure lafiya shi ne fahimtar juna. Mace ta gane abin da mijinta ba ya so ta bari, shi kuma ya yi ƙoƙarin yaba mata a kan kowane abu.”

• Kar a yi hukunci lokacin fushi: Yanke hukunchi lokacin fushi yana samar da nadama a rayuwa idan miji da mata suna cikin fushi kar wani daga cikinsu ya yi wani hukunci. Idan namijin ne ya yi fushi ta ƙyale shi ya huce sannan su yi magana.

Idan ita ce ta yi fushin ya bari ta huce sannan su yi magana. Amma a daina garajen saki, ko garajen kai ƙara wajen iyaye, ko kai ƙara kotu, ko wani wuri.

Abin da Hausawa ke ƙaranci a zaman aure

A al’ummar Hausawa, an fi mayar da hankali kan shirye-shiryen aure fiye da koya wa ma’auratan yadda za su zauna lafiya da juna.

A wannan zamanin ma ana ganin yadda kashe makuɗan kuɗaɗe ya zama abin gadara da alfahari a aure, kama daga shirya liyafa, da kayan lefe, da kayan ɗaki, da kayan gara, da dai sauransu.

Sai dai za a iya cewa babu laifi a baya-bayan nan ana samun ƙaruwar buɗe cibiyoyin gyara zamantakewar aure a sassan yankin.

“Kamar sumbata (kiss), mutane da yawa na ganin ba Musulunci ba ne, ba na Hausawa ba ne. Amma mun fahimta cewa Annabi Muhammdu SAW yakan yi hakan da iyalansa,” a cewar Dr Sadiha Sulaiman, wata da ke shirin amarcewa a lokacin.

“Wasu daga cikin Hausawanmu kuma za ka ga ba su son su fita unguwa da matansu, sai dai direba ya kai su. Wasu kuma ba su son su yi wanka tare da matan nasu,” in ji Amir Tijjani Bawa mai shirin angwancewa a 2020.

“Amma ka ga waɗannan abubuwan na ƙara danƙon soyayya.”

Duka waɗannan na cikin abubuwan da masu shirin yin aure ke koya a cibiyar, wadda shahararren malamin addinin Musuluncin ke gudanarwa.

Share to
You May Also Like
Advertisment